Revelation of John 15

Malaʼiku Bakwai da Annobai Bakwai

1Na ga wata babbar alama mai banmamaki a sama: malaʼiku bakwai da annobai bakwai na ƙarshe-na ƙarshe, domin da su ne fushin Allah ya cika. 2Sai na ga abin da ya yi kamar tekun gilashi gauraye da wuta kuma tsaye kusa da teku, waɗanda suka ci nasara bisan dabbar da siffarta da bisan lambar sunanta. Suna riƙe da garayu waɗanda Allah ya ba su 3suka rera waƙar Musa bawan Allah da kuma waƙar Ɗan Ragon suna cewa:

“Ayyukanka suna da girma da kuma banmamaki,
ya Ubangiji Maɗaukaki.
Alʼamuranka suna da aminci da kuma gaskiya,
ya Sarkin zamanai.
4Wane ne ba zai ji tsoronka,
yǎ kuma kawo ɗaukaka ga sunanka ba, Ya Ubangiji?
Gama kai kaɗai ne mai tsarki.
Dukan alʼummai za su zo
su yi sujada a gabanka,
gama an bayyana ayyukan adalcinka.”
5Bayan wannan sai na duba, a cikin sama kuwa sai ga haikali, wato, Wuri mai tsarki na Shaida, a buɗe. 6Daga cikin haikalin malaʼiku bakwai tare da annobai bakwai suka fito. Suna saye da tufafin lilin masu tsabta masu walƙiya, suna kuma saye da ɗamarar zinariya a ƙirjinsu. 7Sai ɗaya daga cikin halittu huɗun nan masu rai, ya ba wa malaʼiku bakwai nan kwanonin zinariya bakwai cike da fushin Allah, wanda yake raye har abada abadin. 8Aka kuma cika haikalin da hayaƙi daga ɗaukakar Allah da kuma daga ikonsa, kuma ba wanda ya iya shiga haikalin sai da aka cika annobai bakwai nan na malaʼiku bakwai.

Copyright information for HauSRK